ABNA24 : A jawabin da ya gabatar, Patrice Talon ya yi kira ga al’ummar kasar su hada kai domin tabbatar da ci gaban kasa da kuma yaki da talauci.
A cewarsa, babban kalubalen dake gabansu, kuma alkiblar da ya kamata su bi shi ne, ajiye sabanin dake tsakaninsu da mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci da suka hada da karfafa neman ci gaba da hada hannu wajen yaki da talauci, wanda shi ne abokin gabansu baki daya.
Talon ya yi ammana cewa kiran na sa zai ba Benin damar samun wadatar makamashi cikin watanni 30, da samun ruwan sha a fadin kasar zuwa karshen 2023 da karfafa demokradiyya da kyakkyawan shugabanci mai dorewa.
342/